28 Janairu 2025 - 14:20
Jagora: Isra’ila Tasha Kayi Daga Karamin Yakkin Gaza/ Kada Mu Nemi Abota Ta Sirri Da Abokan Gaba

"Tarihin mulkin mallaka yayi nuni akan matakai guda uku ne: "Wawure albarkatun kasa," "Wawure al'adu, da lalata ingantattun al'adu." da "wawashewa yan kasancin kasa da addini na al'ummomi”,wanda a yau, tsarin mulki mai karfi da mugunta na duniya suna anfani da dukkanin matakai uku na mulkin mallaka a kan al'ummai".

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da jami'an gwamnati da jakadun kasashen musulmi

A safiyar yau ne A safiyar yau ne a munasabar zagayowar ranar aiken Manzancin Manzon Allah, Annabi Muhammad Mustafa (SAW). Sayyid Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da shugabannin bangarori uku na gwamnati, da gungu na wasu daga cikin shugabannin gwamnati da jakadun kasashen musulmi, da ma sauran jama'a daban-daban.

A cikin wannan taro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki wannan aike a matsayin wani tsari mai ci gaba da wanzuwa kuma muhimmin darasinsa ga al'ummomin bil'adama musamman musulmi shi ne amfani da hankali da imani wajen samar da sauyi na tunani da fahimta inda ya jaddada cewa: A halin yanzu, yunkurin gwagwarmayar da ta faro tun daga nasarar juyin juya halin Musulunci, wata gaba ce daga gabban aiken annabci da ta hanyar amfani da hankali da imani ta iya farkar da al'ummar musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, wanda da kuma durkusawar gwamnatin sahyoniyawan a gaban Gaza da Lebanon sakamako ne na wannan gwagwarmaya.

Ayatullah Khamenei ya taya al'ummar Iran da al'ummar musulmi da dukkanin masu neman 'yanci da 'yantantu a fadin duniya murnar zagayowar ranar Idil-Mab’as, tare da taya al'ummar Iran murnar zagayowar watan Bahman, wanda yake watan da Juyin juya halin yayi nasara na Musulunci wanda ya kafu daga akan tasirin Mabaath, in da ya kara da cewa: aiken manzanci yana daya daga cikin manya-manyan abubuwan da suka faru a tarihin bil'adama na wancan lokacin da kuma lokutan da suka biyo baya.

Ya anbaci kayan aikin da annabawa guda biyu da suke anfani da shi don haifar da sauyi a cikin al'ummomin mutane wato hankali da imani, sannan ya kara da cewa: Annabawa suna taimaka wa bil'adama wajen samun hanyar ci gaba da tafarki madaidaici ta hanyar farkar da hankali da imani a cikin mutane, kuma da wannan hikimar dalilin ne yasa Al-Qur'ani yake ta maimaitawa batun yin tunani da hankaltuwa da tuntuntuni.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira imani da babban ginshikinsa wato tauhidi, a matsayin tsarin mahangar duniyar musulmi da kuma tushen kafuwar al'ummar musulmi, ya kuma bayyana cewa: aiken manzanci ba abu ne da ya faru kwatsan ko wani lamari ne na lokaci guda ba, da ya kebanta da wata rana ba, sai dai ya ce: a’a tafarki ne mai dorewa, wanda za a iya samun albarkarsa idan mutum ya yi amfani da hankali da imani kuma zai  iya amfani da darussansa a kowane lokaci don haifar da sauyi na hankali da aikace da gyara matsaloli.

Jagora ya kira daya daga cikin muhimman sakonnin aiken manzanci ga daukacin hukumomi da kasashen musulmi bisa yin imani da gaskiyar cewa: “Ga Allah daukaka ta ke” inda ya ce: Ta hanyar dacewa da daukakar Ubangiji, babu wani makiyi ko ma’aikacin waje da zai iya haifar da wani abu mara kyau a Ruhi da ta jiki.

Ayatullah Khamenei ya yi la'akari da mahangar hankali game da abubuwan da suke faruwa a duniya a yau da suke da muhimmanci ga kowa da kowa, musamman jami'an Iran mai girma da kuma Musulunci, kuma a yayin da yake bayani kan tsarin da 'yan mulkin mallaka suke yi na wawure al'ummomin bil'adama ya ce: Tarihin mulkin mallaka yayi nuni akan matakai guda uku ne: "Wawure albarkatun kasa," "Wawure al'adu, da lalata ingantattun al'adu." da "wawashewa yan kasancin kasa da addini na al'ummomi”,wanda a yau, tsarin mulki mai karfi da mugunta na duniya suna anfani da  dukkanin matakai uku na mulkin mallaka a kan al'ummai.

Ya kira gwamnatin Amurka a sahun gaba ta ma'abota girman kai da mulkin mallaka gwamnatin da ke karkashin ikon masu karfin kudi na duniya, inda ya kara da cewa: A kowace rana manyan kungiyoyin hada-hadar kudi suna ta kulla makarkashiya don sauya asali da muradun kasashe da kuma fadada tasirin mulkin mallaka. Kuma kamar yadda Alqur'ani ya fada, suna son duk abin da zai jefa ku cikin wahala.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ayoyin kur'ani mai tsarki da suke nuni da cewa kiyayyar da kyamar da makiya Musulunci su ke da shi acikin kirazansu ya fi abin da su ke bayyanawa a cikin maganganunsu da dabi'unsu, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Kasancewar wakilan majalisar dokokin Amurka suna jinjina tare da tafawa wanda ya yi kisan gilla kuma ya yi sanadiyyar wargaza dubban yara”. Ko kuma yadda suka ba da lambar yabo ga kyaftin din wani jirgin Amurka da ya harbo jirgin fasinja na Iran dauke da fasinjoji 300 a cikinsa, misali ne na mugunyar zuciyarsu da tsabar kiyayya, da muguntar da ke boye a bayan murmushin diflomasiyyarsu, kuma dole ne mu bude idanunmu ga wadannan hujjojin gaskiyar kuma Alkur'ani ya ce, "Kada mu nemi abota ta sirri da su".

Da yake jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan a sa’insar duniya, ya jaddada cewa: Dole ne mu mai da hankali mu kula kan wadanda muke fuskanta da wadanda muke hulda da su da kuma wadanda yin magana da su.

Ayatullah Khamenei ya kira yunkurin gwagwarmayar da ake yi a halin yanzu a matsayin yanki na aiken annabta da ya samu kafuwa daga tasirin juyin juya halin Musulunci na Iran yayin da yake ishara da nasarar da aka samu a zirin Gaza yana mai cewa: Wannan yanki dan karami iyakantacce ya iya kai gwamnatin sahyoniya da ke da makamai wacce ta dogara ga cikakken goyon bayan Amurka durkusawa da gwiwowinsa”. Wannan nasara ta samo asali ne daga yin amfani da hankali da bangaskiya, da danfaruwar zuciyar mutum ga Allah, da kuma gaskata ɗaukakar Allah.

Ya dauki irin tsayin daka da kungiyar Hizbullah ta yi duk da rashin shahidi Nasrallah a matsayin wani misali na bayyanan ne na tsayin daka a wannan zamani da muke ciki, inda ya kara da cewa: shin Manyan mutane nawa ne a duniya da suke a matakin matsayin Sayyid Hassan Nasrallah Rd? Tare da rasa irin wannan shaksiyya, kuma yayin da masoya da makiya suke tunanin aikin Hizbullah ya kare, amma Hizbullah ta nuna cewa ba wai kawai ba ta kare ba ne, a’a wasu lokutan kuma ta tsaya tsayin daka gaban gwamnatin sahyoniyawa tare da karin kaimi.

A farkon wannan taro, shugaba Pezhikian ya bayyana cewa, manufar aiko annabawa ita ce tabbatar da gaskiya da adalci domin kawar da sabani da fadace-fadace, yana mai ishara da aikin farko da Annabi Muhammad ya yi bayan hijirarsa zuwa Madina don samar da ‘yan uwantaka tsakanin kabilun da ke da dadadden bambance-bambance, ya ce: A yau fiye da kowane lokaci, Iran, da al'ummomin Musulunci, da dukkan al'ummomi suna bukatar su yi riko da wannan hangen nesa.

A karshe yayin da yake ishara da laifuffukan da hukumomi suka aikata da kuma zubar da jinin musulmi da yara kanana bisa wasu dalilai daban-daban, shugaba Pezhikian ya yi nuni da cewa: Tare da hadin kai da hadin gwiwar musulmi, za a samar yanayin tabbatar da adalci. Kuma barcin azzalumai zai gagara don ci gaba da yaki da zubar da jini".

Abin da aka kawo anan wa masu sauraro a kasa shi ne "kunshin labarai" da aka buga kawai a gaggauce za’a sake buga bayanan Jagoran juyin juya halin Musulunci a kafar yada labarai ta KHAMENEI.IR da shafofin na hukuma a shafukan sada zumunta, da kuma "cikakken bayani". Ana buga bayanin kalaman Ayatullah Khamenei kamar yadda aka saba, kuma za a buga shi a sashin "Sanarwa" na wannan gidan yanar gizon nan da 'yan sa'o'i masu zuwa.